Add this

Friday, September 6, 2019

Minene z-sip program

ASSALAMU ALAIKUMSalam,...
TAKAITACCHEN BAYANI KAN ZASIP.
Tsari ne aka shirya shi irin tsari na N-Power, tallafi ne ba aiki bane, ba fansho ba Giratuti. Gaba daya Mutu 3800 zaa dauka, matasa Maza da Mata Wanda duk wata Mai girma Gwamna Zai basu 10,000.
Haka kowache karamar hukuma Tanada Coordinators da Supervisors Wanda Mai girma Gwamna ya Aminta da duk wata zai basu 100,000 kowannen su har su Goma 14.
Haka kowache mazaba na da coordinator Guda guda Wanda kowannane su zaa basu 50,000. Sanna akwai kwamiti na jiha Wanda zasu kula da tsarin yadda aikin zai gudana, Sanna akwai kwamitin mu na rikon kwarya Wanda idan mun kammala zamu sakar ma coordinators su chi gaba da gudanar da shirin.
Kowache karamar hukuma zaa iya samun forms ta hannun wadannan wurare domin sune aka raba forms tsakanin su dai dai Gwargwado;-
PDP LG HQtres
Senators
Reps
State Assembly
Traditional Institutions
G8
Stakeholders
Sannan Anbude website (www.z-sip.com.ng) ga Wanda baida hanya ga duka wadannan da aka ba forms shikuma yachika da wayar shi ko kuma yaje gurin da akwai cafe ya chika. Ranar jumaa zaa kammala raba forms da chikewa online.
Zaafitar da sunayen wadanda sukayi nasara chikin sati Mai zuwa, idan kwamiti ya kammala shirye shirye zai kirasu domin tantanchewa.
Baa sayar da form na Z-Sip sai dai duk cafe dakaje chikewa suna da hakkin su chaje ka yadda suke tsarin su.
Kuma ba CAFE Guda kawai ke iya chikewa ba ko ina kaje duk daya ne ko kuma da wayar ka duk zaiyi.
Muna godiya ga Mai girma Gwamna Bello Matawalle domin taimakon Matasa.
Allah ba Mai rabo saa
Allah shi yabbamu
Allah mungode.
Daga Abdulazez Umar Sodangi

Sunday, March 31, 2019

Muhadara :minene hukuncin masu wulakanta alqurani tareda shekh abubakar sodangi  Assalamu alaikum
Ayau insha Allah mun kawo maku Muhadara Daga bakin shekh abubakar Muhammad sodangi mai taken

      
MINENE HUKUNCIN: -

1. Masu wulakanta Qur'ani?
2. Wanda yaggani anyi?
3. Masu yadawa a Facebook, WhatsApp da dukkan social media?

Wannan dama karin bayanai masu yawa sune cikin wannan audio din.
Tare da Sheikh Abubakar Ibn Muhammad Sodangi a karatun na jiya Assabar 22nd Rajab, 1440 AH daidai da 29th March, 2019 a Masallacin Abdullahi Ibn Abbas (Maryam Qur'an Masjid) GRA, Gusau

Kayi downloading a nan 👇👇👇
https://kiwi6.com/file/6w6vydy62t

Monday, March 25, 2019

An fadi ranar Fara jarrabawar waecAssalamu Alaikum
Yan uwa barka da war haka da sake kasancewa da mu acikin wannan page Mai albarka, Inda zamu sanar daku cewa ranar Fara jarrabawar waec ta 2019,
Tuni dai hukumar shirya jarrabawar waec ta sanar da fara jarrabawar waec a 8 ga watan April 2019 insha Allah, kuma zaa Fara da animal husbandry a 11 ga watan April ga daliban da suke karatun ilimin kimiya (science) .Allah Ubangiji ya bamu sa'a.
Ku kasance damu a rubutun mu Na gaba.
Mungode

Saturday, March 9, 2019

Live:sakamakon zaben gwamnoni da yan majalisun jaha

Assalamu Alaikum
Yan uwa Barka da warhaka da sake kasancewa da wannan shafi mai albarka wanda ya Saba kawomaku karance karance hadi da wayarwa Akan internet da kuma bicike ,ayau insha Allah mun samu kawomaku yadda sakamakon zaben gwamnoni da yan majalisun jaha Wanda ya Gudana a ranar assabar 9/march/201,domin kalon yadda sakamakon yake Gudana a fadin jahohin Nigeria sai ka shiga Wannan link dake kasa
👎👎👎👎👎👎👎👎👎


https://www.bbc.com/hausa/resources/idt-28109eb2-5fd2-4b07-875f-792c4fab694e
Allah yasa Ayi Lapiya a Kare Lapiya .
Domin tambaya ko Karin bayani zaku iya turomuna da sako ta hanyar adreshinmu Na G-mail
Iinfo@ausodangi.com.ng
Mungode.
Abdulazez Umar sodangi
CEO at ausodangi.com.ng

Saturday, March 2, 2019

An bude sabon masalacin jumua'ah wanda shugaba muhamadu buhari ya gina

MASHA ALLAH....

Sabon Masallacin Juma'a kenan wanda Muhammadu Buhari ya gina daga kudaden albashinsa dayake dauka duk wata, a unguwar dimilko ya gina Masallacin cikin filinsa na Gado wanda ya gada daga mahaifinsa....

A wannan rana ta Juma'a aka kaddamar da afara amfani da Masallacin inda mai martaba Sarkin Daura ya jagoranci sallar Juma'a ta farko a Masallacin.....

Allah ya saka da Alheri Allah ya karbi tarin ibadun da zaa gudanar a Masallacin daga yanzu har zuwa ranar karshe....

Anyi ingantaccen ginin da zaa dade ana amfana, an saka kayayyakin zamani da zaa samu nutsuwa sosai yayin gudanar da ibada......

Monday, February 25, 2019

(Download)Huduba ta 3 akan wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma tareda shekh Ahmad ibn Umar KanomaAssalamu Alaikum 
Munama masu karanata Wannan rubutu fatan alheri tare da fatan suna jin dadin kasancewa damu, 
Ayau insha Allah zamu kawo maku Huduba ta 3 akan wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma tareda shekh Ahmad ibn Umar Kanoma Abu Abdullahi (hafizahullah),Alokacin da yake gabatar da Hudubar jumuah mai taken wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma da musibar da zata cimma Mai wulakantashi wadda ta Gudana a masalacin umar ibn hadaf 16 jimada thani 1440 daidai da 22/2/2019.
Domin saukar da wannan karatu acikin Wayyarka sai ka shiga Wannan link dake kasa 
👎👎👎👎👎👎👎👎

Ayi sauraro lapiya  mun gode 
Domin tambayata ko shawara zaku iya turomuna da sako kai tsaye a adireshinmu na G-mail 
Ko ku kiramu a wannan number 

(LIVE) SAKAMAKON ZABEN SHUGABAN KASA A COLLECTION CENTER ABUJA

assalamu alaikum
A Yanzu haka ana shigaba da fadin sakamokn zaben shugaban kasa a babban birnin tarayya Abuja a (collection center) Inda aka fadi sakamokon jaha biyu ekiti da osun Inda jamiyar APC ta samu nasara, idan kana bukatar cigaba da karanta cikaken sakamakon sai ka shiga Wannan link dake kasa 👎👎👎👎👎👎👎👎
https://www.bbc.com/hausa/resources/idt-b44969c9-b432-4a48-8b89-876d65be16e3
Fatar mu Allah yasa Agama Lapiya
Mungode 

Sunday, February 24, 2019

AN KAMMALA FASSARAR LITTAFAN PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATHICS ZUWA HARSHEN HAUSA.Asslam alaikum 
Muna godiya ga Allah subahanahu     wata'ala,
A yau insha Allah zamuyi magana Akan kamala fasssrar littafan chemistry physics, mathematics zuwa harshen hausa Wanda cibiyar bincike kan harsunan Nigeria da fasssra da hikimomin Al umma dake jami'ar bayero kano  university (B U K), 
Wannan cibiya ta dake bayero university dake birnin kano tayi nasarar bugawa tare da fassara littafan kimiya guda takwas zuwa Yaren Hausa saboda daliban firamare da kuma karamar sikandarari (junior section) da kuma babbar sakandari (senior section) saboda dalibai yan yankin arewacin Nigeria, 
Shugaban Wannan cibiya farfesa Aliyu mua'zu yace littafan sun hada da :
1,kimiya da fasaha Don makarantun firamare,litafi Na daya zuwa na ukku 
2,Lisafi don kananan makaratun sakandari, Littafi Na daya zuwa na ukku, 
3,Fizis (physics) don Mayan makarantun sakandari, 
4,Kyamistiri (Chemistry) don manyan makaratun sakandari .
Waddanan Sune littafan da aka fassara zuwa Hausa. 
Haka kuma Alokacin gudanar da wannan aiki shima farfesa Mu'azu yace sunyi amfani ne da tsarin karantawa Na kasa (National curriculum) tareda taimakawar aboakan aikinsu na faculty of education da kuma faculty of science, 
A karshe kungiyar ta arewa (sof)  Tana Kira ga dukkanin hukumomomin jihohi Dana tarayya da su amince da yin amfani da wadannan littafan a makarantunmu Don haifar da kwararun likitoci da injiniyoyi da sauransu. 
Ubangiji Allah yasaka masu da Alheri.

Friday, February 22, 2019

(JAMB 2019)ABUBUWA 19 DA AKA HANA SHIGA RUBUTA JARABAWAR JAMB DASU.
Assalamu alaikum
A yau insha Allah zamuyi magana Akan abubuwa 19 da aka hana shiga dasu wurin rubuta jarabawar jamb, ya kamata ga Wanda zai yi jarabawar jamb a wannan shekara ya gujewa waddanan abubuwan da zan kawo, domin zasu iya hana mutum yaki rubuta jarabawar,
Abubuwan da aka hana a shigo dasu wurin jamb gasu kamar haka :
1.Agogon hannu
2.Biro
3.Handset ko makamancinsa
4.Glas na ido na musaman!
5.Calculator
6.USB,CD,FLASH ko makamantansu
7.Littafi ko waninsa
8.Camera
9.Abub recording
10.Microphone
11.Earpiece
12.Biro Mai karanta rubutu
13.Smart lenses.
14.Smart ring/jewellery
15.Smart buttons
16.key holder
17.ATM card
18.Abin goge rubutu
19.Bluetooth Device
Da sauran su.
Allah Ka bamu sa'a baki daya amin.

Wednesday, February 20, 2019

YADDA AKE SAUKE VEDIO A FACEBOOK.


assalamu alaikum
A yau Zamuyi magana Akan yadda ake sauke vedio a facebook,
Kamar yadda muka sani facebook wurine Wanda ya kunshi mutane da dama kama Daga yan uwa, abokai da sauransu, Wanda zai ba mutum damar magana da dan uwansa ta hanyar rubutu ko vedio ko photo, sauda yawa zaka ga mutum ya ci Karo da vedio acikin facebook Amma bai San yanda zai yi download nashi ba, to insha Allah yau Zamuyi bayani yadda ake dauko vedio a cikin facebook, hanya mafi sauki wurin sauke vedio a facebook shine kayi amfani da browser ta kamfanin #Google wato goggle chrome, ga hanyar da zaka bi :da zarar kaje kan vedion da kake son daukowa zai baka alamar download kamar yadda kuke gani a #youtube sai ka Dane vedion Shikenan zai sauke kan Wayyarka.
Hanya ta biyu Akwai application a play store Wanda zaka iya daukowa suma suna baka damar ka sauke vedion zuwa cikin Wayyarka.
Mungode sosai.
Zaku iya Turomuna sako ta adireshinmu na G mail
Info@ausodangi.com.ng

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Minene z-sip program