Monday, December 31, 2018

shin ko Kasan makomar masalacin qudus?

Ana ci gaba da rigima  tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da masallacin Kudus, daya daga cikin wuraren da suka fi ko wanne jawo ce-ce-ku-ce a gabas ta tsakiya.ga yadda abun ya kaya Ayi karatu Lapiya.
Birnin Kudus na da muhimmanci ga addinin Yahudawa da na Kiristoci da kuma na Musulmi, addinai ukun da ke da nasaba da Annabi Ibrahim (AS).
Kudus- Suna ne da yake da jan hankalin Musulmi da Kiritoci da Yahudawa a daruruwan shekarun da suka shafe suna zama tare da kuma ce-ce-ku-ce kan birnin.
A harshen Yahudanci ana ce wa birnin Yerushalayim kuma a Larabci ana ce masa al-Quds, yana daga cikin biranen da suka fi dadewa a tarihi.
Sau da yawa an ci birnin da yaki tare da lalata shi.
Kazalika an sake gina shi sau da yawa. Ko wanne mataki na kasan birnin na dauke da wani bangare na tarihin birnin Kudus.
Duk da cewar duk birnin ne silar daya daga cikin abubuwan da suke jawo ta da jijiyar wuya tsakanin mabiya addinan uku, dukkansu sun yi tarayya kan girmama wannan wuri mai tsarki.
Tsohon birnin Kudus yana tsakiyar birnin ne a yanzu inda kwararo-kwararo masu yawa da kuma tsarin gine-gine na tarihi sun bambance bangarorin Kiristoci da na Musulmai da na Yahudawa da kuma na Aarmeniyawa.
Tsohon birnin yana kewaye ne da wata ganuwa mai kama ta dutse kuma tana dauke da wasu wurare mafiya tsarki ga al'ummun duniya.
Ko wacce unguwa na wakiltar al'ummarta ne. Kiristoci na da unguwanni biyu saboda Armeniyawa ma Kiristoci ne kuma unguwarsu - wacce ta fi kankanta cikin hudun - daya ce daga cikin tsofafin cibiyoyin Armeniyawa a duniya.
Wani abu ne na daban saboda al'ummar Armeniyawa sun adana al'adarsu cikin Majami'ay St James wadda ta kunshi da yawa daga cikin unguwarsu.
Majami'ar
A cikin unguwar Kiristoci akwai Majami'ar da ake ce wa Church of the Holy Sepulchre a turance, wadda take da muhimmanci ga Kiristoci a fadin duniya. Majami'ar na wani wuri da aka yi imanin cewar yana da alaka da  labarin Annabi Isa (AS).
Da yawan Kiristoci sun yi imanin cewar an gicciye Annabi Isa ne a wurin nan tsaunin Golgotha, ko kuma tsaunin Calvary, inda suka yi imanin cewar inda aka binne shi yana wajen da ake ce wa sepulchre din, kuma ta nan ne suka yi imanin cewar ya tashi.
Wakilai daga majami'u daban-daban, ciki har da Cocin Girka da ta darikar Katolika da ta Armeniyawa da ta Kibdawa ne suke gudanar da lamuran cocin.
Majami'ar daya ce daga cikin wuraren ibada ga miliyoyin Kiristoci da ke zuwa bauta inda suka yi imanin cewar an bunne Annabi Isa (AS) domin neman kwanciyar hankali da kuma tabarruki da addu'a a wurin.
Masallacin
Unguwar Musulmai ita ce unguwa mafi girma daga cikin unguwanni hudu kuma a cikinta akwai Qubbat al-Sakhrah da massalacin Al-aqsa da ke kan wani tudu wanda Musulmi suka fi sani da Haram al-Sharif, ko kuma wuri mai tsarki.
Masallacin shi ne masallaci na uku a tsarki cikin addinin Musulunci kuma yana karkashin gudanarwar wani kwamitin amintattu da ake kira Waqf.
Musulmi sun yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya taho nan daga Makka a daren.
To Allah ya Kyauta.
www.ausodangi.com.ng

Takaitacen tarihin sheikh abubakar Muhammad sodangi


Assalamu alaikum
Yan uwa barka da warhaka ,
Wannan shine Takaitacen tarihin shekh abubakar Muhammad sodangi :
An haifi malam abubakar Muhammad sodangi a garin gusau, kuma ya Fara karatunsa a garin gusau da Zaria, Inda yayi karatun alqurani ga hannun mahaifinsa malam  Muhammad sodangi da kuma kawunsa  malam aliyu abdullahi shiyar mayana gusau, bayan haka ya cigaba da neman ilimin addinin musulunci acikin fannoni da dama a wajen Malamai mabanabanta Daga cikin malamansa Akwai malam  Suleiman Mai yara kofar jange gusau da malam lawali Mada kofar Mani gusau da malam Muhammad rijiyar sarki gusau  da malam sani Dan Fulani sokoto  da Liman isah shuraihu tudun Wada gusau da malam sa'adu na'ibi kanwuri gusau da malam umaru Na ruwan doruwa,
Haka kuma a birnin Zaria yayi karatu a wajen malam Muhammad unguwar magajiya da mlm saadu madunki kofar kudu da alarama abdullahi.
Malam abubakar ya karanci fannonin ilimi daban -daban ga waddanan Malamai da wasunsu kamar :tajwidi,tauhidi,hadisi, nahawu da usulul fiqhi,da luggar larabci, da balaga da mandiki da tarihi da hisabi da ilimin adabi da tafsirin alqurani Mai girma da ilimin fakaqi da sauransu.
Kuma a bangaren ilimin zamani mlm abubakar sodangi yayi karatun primary a garin morai t/mafara kuma yayi karatun babban certificate ta ilimin larabci, Hausa da turanci a cibiyar (Sara)  a karkashin jami'ar Usman Dan fodiyo a reshenta dake FCET gusau.
A bangaren rubuce rubucen litafan addini da sauransu mlm abubakar Muhammad sodangi ya rubuta litafai da dama masu alaka da ilimin ibada da zamatakewa da tarbiya da da tarihi da tattalin arziki da siyasa da ilimin fakaqi da sauransu.
Yanzu haka kuma mlm abubakar Muhammad sodangi yana rike da mukamin daraktan makarantar mlm Muhammad sodangi kuma shugaban cibiyar nazarin suyasar musulunci ta jahar zamfara, kuma shine Parmanet commissioner zamfara state shariah and research and development commission, kuma yana daya Daga cikin naibban kinmin masalacin jumuah na shekh abubakar Mahmud gummi (Rabiah gusau) Wannan shine Takaitacen tarihin shekh abubakar Muhammad sodangi.
Masha Allah barakallah.
Ku kasance damu akowane lokaci
Domin tarihi na manyan malamai  hadi da wayarwa Akan internet.
Masha Allah barakallah.

Mungode.
Info@ausodangi.com.ng

Shin ko kasan zaka iya bude bank account acikin facebook.

Mai karatun barka da warhaka da fatan kana jin dadin kasancewa damu.
kasancewar al'amarin wannan duniya ta fuskar fasaha kullun kara gaba yake.
A yau munzo muku da yadda zaka bude asususn ajiya na banki wato bank account ta facebook, wannan fasahar da zata bawa mai amfani da shafin sada zumunta na facebook damar bude asusun ajiya na banki cikin kasa da mintuna biyar 5 kacal ba tare da kaje banki ba.
YADDA ZAKA  BUDE  ACCOUNT DIN;
Nasan da dama masu amfani da facebook messenger kan ci karo da tallan bankin UBA wato UBA catting bank ?
yadda zaka yi shine;
zaka bukaci yin hira da da shi bankin wato ''chat'' kana dannawa LEO zai maka marhaba sannan ya tambayeka mi kake da bukata ,a

Shin ko kasan zaka iya karatu a wayarka ta online.

Assalamu alaikum
Inamaku fatan alheri da fatan kuna Lapiya kamar yadda aka sani cewa Yanzu duniya ta koma google ko nace online Yanzu ko siyayya zakayi zaka iya zuwa online kasiya idan kanason duba admission ko Kayi registration shima online ne
To shima Yanzu karatu ma zaka iya yin sa online ba tare da ko sisi ba, kuma idan Ka gama za'abaka certificate na shedar cewa kayi karatu  kuma ana yin diploma da sauransu,

Ga mai bukata sai tayi gaugawa ya shiga cikin browser tai ya rubuta www. Alison. Com idan ya Bude sai ya shiga apply for online study Amma yazama dole Kanada gmail account kuma yazama kana shiga a kai a Kai saboda suna amfani da yadda kake shiga, kuma Duk bayan lokaci ana yin test domin a gano cewa kana ganewa, kuma Akwai exam idan Ka gama karatunka zaka rubuta,
Kuma abun namaki zaka iya karatun ko wane subject Tun Daga ilimin computer 💻 Mai 'kwa'kwalwa , da ilimin falsafa (philosophy) da english da sauransu
ku kasance tare da mu a wannan kafa ta . www.ausodangi.com.ng

SHIN KO KASAN ZAKA IYA GANO NUMBOBINKA NA LAYIN KA DA YA BACE ACIKIN FACBOOK.

Assalamu alaikum
Shin ko kai maabuci shiga facebook ne to ga dama ta adana numbobi a facebook ba tare da ko sisi ba ,
bugu da kari ma zaka iya gano numbobinka da suka bace a shekarun baya acikin facebook idan dai har kana da account na faceebook,
hanyoyin dawowa da numbobinka da suka bata ko wayyar ta bata ko layinka ya bace gasu kamar haka;
1-yazama ka iya amfani da facebook sosai
2-yazama kana da  facebook account
3-yazama kana da facebook lite app domin yafi saukin shaani
amma kuma kowane facebook app yanayi
ga hanyar da zaka bi mafi sauki da zaka dawowa da numbobinka cikin sauki a facebook
idan ka shiga facebook sai ka ka duba da kyau sai ka shiga setting sai ka duba zaka ga ansa imported contact sai ka shiga idan ya bude zaka ga anyi wani rubutu mai yawa sai kayi kasa kadan daga nan zaka ga numbobinka gaba daya sai  ka shiga show contact information shikenan sai ka dauko numbobinka .
muna godiya yan uwa ku shi gaba da bibiyar ausodangi.com.ng domin kawo maku bayanai  na tarihi da bincike akan internet.

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Minene z-sip program