Monday, February 25, 2019

(Download)Huduba ta 3 akan wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma tareda shekh Ahmad ibn Umar KanomaAssalamu Alaikum 
Munama masu karanata Wannan rubutu fatan alheri tare da fatan suna jin dadin kasancewa damu, 
Ayau insha Allah zamu kawo maku Huduba ta 3 akan wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma tareda shekh Ahmad ibn Umar Kanoma Abu Abdullahi (hafizahullah),Alokacin da yake gabatar da Hudubar jumuah mai taken wajabcin kiyaye Al Qur'ani Mai girma da musibar da zata cimma Mai wulakantashi wadda ta Gudana a masalacin umar ibn hadaf 16 jimada thani 1440 daidai da 22/2/2019.
Domin saukar da wannan karatu acikin Wayyarka sai ka shiga Wannan link dake kasa 
👎👎👎👎👎👎👎👎

Ayi sauraro lapiya  mun gode 
Domin tambayata ko shawara zaku iya turomuna da sako kai tsaye a adireshinmu na G-mail 
Ko ku kiramu a wannan number 

(LIVE) SAKAMAKON ZABEN SHUGABAN KASA A COLLECTION CENTER ABUJA

assalamu alaikum
A Yanzu haka ana shigaba da fadin sakamokn zaben shugaban kasa a babban birnin tarayya Abuja a (collection center) Inda aka fadi sakamokon jaha biyu ekiti da osun Inda jamiyar APC ta samu nasara, idan kana bukatar cigaba da karanta cikaken sakamakon sai ka shiga Wannan link dake kasa 👎👎👎👎👎👎👎👎
https://www.bbc.com/hausa/resources/idt-b44969c9-b432-4a48-8b89-876d65be16e3
Fatar mu Allah yasa Agama Lapiya
Mungode 

Sunday, February 24, 2019

AN KAMMALA FASSARAR LITTAFAN PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATHICS ZUWA HARSHEN HAUSA.Asslam alaikum 
Muna godiya ga Allah subahanahu     wata'ala,
A yau insha Allah zamuyi magana Akan kamala fasssrar littafan chemistry physics, mathematics zuwa harshen hausa Wanda cibiyar bincike kan harsunan Nigeria da fasssra da hikimomin Al umma dake jami'ar bayero kano  university (B U K), 
Wannan cibiya ta dake bayero university dake birnin kano tayi nasarar bugawa tare da fassara littafan kimiya guda takwas zuwa Yaren Hausa saboda daliban firamare da kuma karamar sikandarari (junior section) da kuma babbar sakandari (senior section) saboda dalibai yan yankin arewacin Nigeria, 
Shugaban Wannan cibiya farfesa Aliyu mua'zu yace littafan sun hada da :
1,kimiya da fasaha Don makarantun firamare,litafi Na daya zuwa na ukku 
2,Lisafi don kananan makaratun sakandari, Littafi Na daya zuwa na ukku, 
3,Fizis (physics) don Mayan makarantun sakandari, 
4,Kyamistiri (Chemistry) don manyan makaratun sakandari .
Waddanan Sune littafan da aka fassara zuwa Hausa. 
Haka kuma Alokacin gudanar da wannan aiki shima farfesa Mu'azu yace sunyi amfani ne da tsarin karantawa Na kasa (National curriculum) tareda taimakawar aboakan aikinsu na faculty of education da kuma faculty of science, 
A karshe kungiyar ta arewa (sof)  Tana Kira ga dukkanin hukumomomin jihohi Dana tarayya da su amince da yin amfani da wadannan littafan a makarantunmu Don haifar da kwararun likitoci da injiniyoyi da sauransu. 
Ubangiji Allah yasaka masu da Alheri.

Friday, February 22, 2019

(JAMB 2019)ABUBUWA 19 DA AKA HANA SHIGA RUBUTA JARABAWAR JAMB DASU.
Assalamu alaikum
A yau insha Allah zamuyi magana Akan abubuwa 19 da aka hana shiga dasu wurin rubuta jarabawar jamb, ya kamata ga Wanda zai yi jarabawar jamb a wannan shekara ya gujewa waddanan abubuwan da zan kawo, domin zasu iya hana mutum yaki rubuta jarabawar,
Abubuwan da aka hana a shigo dasu wurin jamb gasu kamar haka :
1.Agogon hannu
2.Biro
3.Handset ko makamancinsa
4.Glas na ido na musaman!
5.Calculator
6.USB,CD,FLASH ko makamantansu
7.Littafi ko waninsa
8.Camera
9.Abub recording
10.Microphone
11.Earpiece
12.Biro Mai karanta rubutu
13.Smart lenses.
14.Smart ring/jewellery
15.Smart buttons
16.key holder
17.ATM card
18.Abin goge rubutu
19.Bluetooth Device
Da sauran su.
Allah Ka bamu sa'a baki daya amin.

Wednesday, February 20, 2019

YADDA AKE SAUKE VEDIO A FACEBOOK.


assalamu alaikum
A yau Zamuyi magana Akan yadda ake sauke vedio a facebook,
Kamar yadda muka sani facebook wurine Wanda ya kunshi mutane da dama kama Daga yan uwa, abokai da sauransu, Wanda zai ba mutum damar magana da dan uwansa ta hanyar rubutu ko vedio ko photo, sauda yawa zaka ga mutum ya ci Karo da vedio acikin facebook Amma bai San yanda zai yi download nashi ba, to insha Allah yau Zamuyi bayani yadda ake dauko vedio a cikin facebook, hanya mafi sauki wurin sauke vedio a facebook shine kayi amfani da browser ta kamfanin #Google wato goggle chrome, ga hanyar da zaka bi :da zarar kaje kan vedion da kake son daukowa zai baka alamar download kamar yadda kuke gani a #youtube sai ka Dane vedion Shikenan zai sauke kan Wayyarka.
Hanya ta biyu Akwai application a play store Wanda zaka iya daukowa suma suna baka damar ka sauke vedion zuwa cikin Wayyarka.
Mungode sosai.
Zaku iya Turomuna sako ta adireshinmu na G mail
Info@ausodangi.com.ng

Tuesday, February 19, 2019

YADDA AKE AJE NUMBOBIN WAYA AKAN G-MAIL.


Assalamu alaikum
Inama masu karanata Wannan rubutu fatan alheri, kamar yadda kuka sani Yanzu lokacine da mutum yake iya rasa wayarsa a kowane lokaci, abu na biyu zaka ga mutum ya na biyan kamfanin MTN kudi Duk wata suna ciremai kudi da sunan backup, to insha Allah wannan page Mai albarka zai nunamaku yadda mutum zai aje numbobin wayyarsa ba tare da ko sisi ba, cikin mintuna kalilan, Abu na farko ya zama Kanada data acikin wayarka,Abu na biyu yazama G-mail dinka yana saman Wayyarka :
Da farko kaje kan contact dinka maana wurin Numbobinka,zaka ga wani aro can saman numbobinka  kamar haka ➖,bayan Nan zaka ga ansa import and export sai ka shiga ciki ga Misali  a wannan photon dake kasa
Sai ka shiga import /export ,bayan ka shiga zai nunamaka wani wuri Inda yake tambayarka shin kanaso kayi copy Daga layinka zuwa kan G-mail dinka abunda zakayi shine sai kayi ticket Akan layin da numbobinka suke ciki ga Misali acikin wannan photo

Bayan Nan sai kayi ticket Akan layin da numbobinka suke ciki bayan kayi ticket sai kayi kasa zaka ga next ,to Daga Nan zai kawoka Inda zakayi paste ma'ana Inda zaka aje numbobinka sai kayi ticket Akan G-mail dinka ga Misali acikin wannan photo

Bayan kayi click a G-mail naka sai kayi kasa kadan zaka ga next sai ka shiga bayan ka shiga sai matakin karshe ,zakaga numbobinka gaba daya abunda zakayi shine Ka Danna select all ga Misali acikin wannan photo
Bayan kayi mark all sai  kayi kasa kadan zaka ga OK sai ka danna OK, shikenan numbobinka sunyi copy Akan G-mail dinka .
Mungode, idan Akwai Mai tambaya zai iya turomuna ta wannan G-mail
Info@ausodangi.com.ng

Sunday, February 17, 2019

(AUDIO) HUDUBA AKAN WULAKANTA AL QURANI MAI GIRMA TAREDA SHEKH AHMAD IBN UMAR KANOMA

Assalamu Alaikum
Wannan huduba mai taken wulakanta Alqurani mai girma ta gudana a ranar jumuah 9 ga watan jimada thani 1440 masalcin malam ahamd ibn umar kaoma ,domin sauakar da wannan karatu sai ka shiga wannan  link da ke kasa👎👎👎👎👎👎
https://kiwi6.com/file/dw1v6w40rt
Ayi sauraro lapiya.
Ya ubangiji duk masu sa hannu acikin wulakantar ds alqurani Allah ya tona masu asiri,Ya ubangiji kada ka kama mu da abunda wawaye daga cikin mu suke akatawa,,kasa mu cika da imani amin.

Mungode.

YADDA ZAKA DAKATAR DA GANIN HOTUNAN BATSA A FACEBOOK

Assalamu alaikum
Yan uwa Barka da sake kasancewa damu acikin wannan website Mai albarka wanda yake kawo maku abubuwan da suke ci maku tuwo a kwarya Akan internet, yau insha Allah zamu kawo maku yadda mutum zai dakatar da ganin hotunan batsa a facebook,
Wannan matsalar ta cin Karo da hotunan batsa a facebook ta Dade Tana ci muna tuwo a kwarya, saboda zaka ga mutum yana son ya shiga facebook Amma yana jin tsoron shiga saboda bai San irin hotunan da zai ci Karo da su ba, maganar Gaskiya babu wani wuri da mutum zai shiga ya dakatar da ganin wadannan hotunan cikin lokaci daya, amma Akwai Hanyoyin da mutum zai bi,
Hanyoyin da zaka bi Sune :
1,kada Ka kuskura kayi like ko comment Akan Duk irin waddan hotuna.
2,kayi unlike Na shafunka da kaga suna yada irin wadannan hotuna.
3,kayi blocking din Duk Wanda kaga yana yada su.
4,ka fita Daga Duk wani Group da kaga suna talata waddan hotuna.
5,Idan kuma akayi tagging dinka to kayi reporting dinsu a facebook.
Zan dakata anan mu hadu a rubutu Na gaba Mai taken yadda zaka dakatar da download  kai tsaye Na hotuna ko video a whatsapp

KA NEMA YANZU BANKIN FIRST BANK YANA NEMAN MA'AIKATA.

 Wannan  yana neman ma'aikata yanzu haka,duk da cewa Wannan banki yana da rassa a fadin duniya kamar faransa,London,Ghana,Gambia,Gunea,Sierraleone,Senegal,haka kuma suna da babban office a birnin Johannes burg, Beijing da Abu Dhabi,
Wannan banki yana neman ma'aikata yanzu haka a nan Nigeria Daga cikin jihohin da ake bukata sun hada da Birnin tarayya Abuja, Zamfara, kano, Bauchi, Benue, katsina, Sokoto, Gombe, Adamawa, Kaduna,Plateu,Kogi,Borno,Niger,Lagos.
Domin yin register sai ka shiga Wannan link dake kasa  //firstbanknigeria.taleo.net/careersection/fbnex/jobdetail.ftl?job=1900000T


Saturday, February 16, 2019

TSOHON DAN KWALLON NIGERIA OKOCHA YA MUSULUNTA.

Assalamu alaikum
Babban tsohon dan kwallon Nigeria JJ OKOSHA ya bayana cewa ya amshi musulunci, kuma ya zabarma kansa suna Muhmmad saboda ya samu albarkar wannan suna.
Kamar yadda aka sani Okocha babban Dan kwalone a tarihin Nigeria Na alfahari dashi Amma Yanzu Alhamdulillah ya samu shigowa cikin  addinin musulunci,kuma ya musulunta a kasar turkey Inda ya buga wasa tai ta karshe. Wannan sanarwa ta biyo bayan shafukan Sada zumunta na kasacen larabawa.
Allah ya tayashi rikon wannan amana amen.
Mungode sosai ku cigaba da kasancewa tare da wannan Dan dali Mai albarka domin kawo maku bayanai Akan abunda ya shafi tarihi, bincike da kuma duniyar fasaha. 

YADDA ZAKA SAMU DATA 1GB A LAYIN 9MIBILE A NAIRA DARI BIYU KACHAL #200.
Assalamu alaikum
Ayau zanyi magana Akan yadda ake samun data 1GB Akan naira Dari biyu #200.
Amma ga masu amfani da layin 9mibile.
Amma kuma Wannan data kwana 3 take yi kafin ta Kare maana tayi (expire).
Kafin mutum ya shiga Wannan tsarin a naso layinsa ya kasance ya Kai shekara daya yana amfani dashi
Idan kanason Ka tabbatar layinka ya na yin Wannan tsari sai ka danna waddanan numbobi *929*10#,idan ba zai yiba zasu tura maka sako kamar haka,
Sorry this data plan is not available to you for purchase.,har zuwa karshe,
Idan kuma zaiyi ga sakon da zasu turoma,
Dear customer Your request was not successful due to insufficient balance please recharge and try again.
Bayan Nan sai ka saka Katinka Na #200 sai kasaka waddanan numbobi *929*10#,shike Nan zaka samu 1GB data. Enjoy your data.
Mungode.

Wednesday, February 13, 2019

SHIGA KA CIKA TSARIN N POWER MAI TAKEN N -BUILD PROGRAMAssalamu alaikum 
Maraba da zuwa wannan shafi mai albarka domin cika tsarin N Power mai taken (N-build) 
Wannan portal an budeshi a 13 ga Wannan wata na biyu, kuma bada jimawa ba zaa rufe, Domin shika wannan tsari Na N-Power sai ka shiga Wannan link dake kasa 
👎👎👎👎
mun gobe 
Allah ya bada sa'a yasa a samu nasara. 
Wannan tsari Na koyon sanaa Ne, abunda ya shafi 
Gyaran wayya 
Aikin asibiti 
Gyaran wuta
Gyaran Fan fanfo
Da Dai sauransu. 

Tuesday, February 12, 2019

TSOKACINA A KAN KALAMAN SEN: RABI'U KWANKWASO (DR IBRAHIN ILYASU.


Tsokacina A Kan Kalaman Sen. Rabiu Kwankwaso !

Bayan na saurari munanan Kalaman Senator Rabiu Kwankwaso a kan wasu Malaman Sunnah da ya samu sabani da su, ina da tsokaci kamar haka:

1. Da farko, ina so me karatu ya sani, bani da personal sabani da Kwankwaso, kuma ina da dalibai da yawa da aminai masu bin kwankwasiyyah, wasu ma na kusa da shi ne sosai, wasu ma har abinci suna ci tare. Hakanan bani da wata alaka da Gov Ganduje ko Mal Salihu Takai, ko da yake ina da dalibai da abokai zagaye da su.

2. Lallai Senator Kwankwaso Shugabane Jarumi (Strategist), a matsayinsa na tsohon Gwamna har sau biyu a Kano, wanda ya rike manyan mukamai a tarayya, babban dan siyasa ne me dinbin mabiya da tasiri a jaharsa da ma kasa. Jagora ne da ya taimaki yayan talakawa musamman  a cikin mulkinsa karo na biyo, akwai dalibaina da yawa wadanda ba 'ya'yan kowa ba ne amma sun samu damar karo karatu a Malaysia da wasu kasashen duniya a dalilinsa, wannan abu ne da ya kamata a yaba masa a kai.

3. Sai dai kuma lokaci-lokaci Sen. Kwankwaso ya kan saki baki ya furta wasu kalamai a zahiri na Izgilanci ne ga Sunnah dama  addini gaba daya: misali lafuzzan da yayi kwanan a kan Gemu, da Dage Wando, saboda ya samu sabani da wasu Malaman Izala. Babu shakka lafuzzan bai kamata su fito daga bakin Shugaba me tarbiyyar alummah ba!

4. Idan Kwankwaso yana yin raddi ne ga Malaman da ya samu sabani da su, me ya hana ya tsaya akansu su kadai, don me ya tsallaka yayiwa Gemu da dage Wando izgilanci.

5. Babu shakka Masu Kishin addini za su ga wannan  izgili  ne ga Sunnah da ma addini gaba daya. A baya ma, Kwankwaso yayi sakin baki ga Annabi SAW da mahaddata Qurani, lokacin yana kan mulki.

6.Hakika, duk yanda kaso ka kyautata wa Kwankwaso zato ze yi wuya kace Malaman addini suna da girma a idonsa, kasancewar shine Gwamna na farko da ya dauko Dan Siyasa yaronsa  mara alaka da ilmin addini kwata-kwata, ya bashi me bada shawara akan harkar addini, a gari kamar Kano. Hakika, wannan cin fuska ne ga addini da Malaman addini. Ko da yake Gov Ganduje ya ci gaba da rikeshi domin biyan bukatarsa ta siyasa.

7. Ba Kwankwaso ka dai ba, so da yawa, wasu mutane kan jefi Malaman addini da Kalmar "kwadayi". Sai dai an manta, yanayin Kasarmu na "secularism" da rashin mutunta addini da masu yi masa hidima yasa malamai kan shiga wahala saboda rashin albashi daga Gwamnati da kuma tallafi daga mabiya, duk da cewa lokacinsu da zasu je su nemi abinci shi suka sadaukar suka baiwa alumma, wajen; Jagoranci, Limanci, Khutubah, lecture, Programs, a Radio da sauransu. Sabanin a sauran kasashen duniya inda Malamin addini ke samun cikakkiyar kulawa, Gaida, albashi, mota, da sauransu. Amma anan dan siyasa da ya dau kudin alumma ya gina kansa da iyalinsa, da sauran ma rasa gane alamura, su ne zasu rinka yiwa Malamai gori, domin sun basu kudi, tunda su ba yan kasa bane, basu da hakki a dukiyar kasa.

8. Lallai akwai Malamai na Izala da na Dariqah masu rashin Qana'a da wadatar zuci wadanda suke abinda bai daceba na kwadayi da zubar da kimar ilmi, ya wajjaba su daina su martaba ilminsu da darajarsu.
 ÙˆÙ„Ùˆ ان اهل العلم صانوه صانهم. .. ولو عظموه في النفوس افظما

9. Tabbas Kwankwaso ya lura mabiyan Malaman Dariqah sun fi zafi da karsashi  wajen  kare Malamansu shi yasa bai taba yi musu irin wannan kakkausan sukan ba. Daliban Sunnah kalubalenku!

10. Akwai fitattun 'Yan Siyasa irinsu Musa Ilyasu Kwankwaso wadanda suka shahara wajen cin Mutuncin Sen Kwankwaso a kullum a Radio, da kuma shahararrun mawaka irinsu Rarara Wanda a wakarsa ya ke cin mutuncin Kwankwaso da kalmomi masu muni irinsu: Tsula, Biri, Jan Gwalagwada. Abin mamaki ban taba jin yafito yai musu kakkausan raddi ba, sai Malaman sunnah.

11. Ina bada shawara ga Sen Kwankwaso ya tuba ga Allah kuma ya nemi afuwa kuma ya shirya tsakaninsa da Malaman Sunnah, sannan ya rinka tauna magana Kafin ya fade ta, a matsayinsa na jagora me dinbin Mabiya. Makusantansa su rinka nuna masa hadarin yin tabargaza da izgilanci ga addini domin kafircine kuma muna funci ne.

قل ابالله وآياته ورسوله كنتم تستهزءون لاتعتذروا قد كفرتم بعد ايمنكم

12. Daga karshe, ko waye mutum,  komai daukakarsa in dai zai taba addini, to Allah zai yi maganinsa, domin shine zai shiga fadan. Kuma bukatar me irin wannan ba zata biya ba, kuma makiyansa sai sunga bayansa.

من عادى ليا فد.آذنته بالحرب

إن الله يدافع عن الذين آمنوا إن الله لايحب كل خوان كفور.
أذن للذين يقتلون بأنهم ظلموا وإن الله على نصرهم لقدير

Allah muna rokonka ka tsare mana imaninmu.

Dr Ibrahim Ilyasu
12/2/2019

DAN NIGERIA YA KAFA TARIHI.

DAN NIGERIA YA KAFA TARIHI

Professor Dr. Idris Ahmed Phd Cryptology Maigidana kuma Masoyina dan Nigeria haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya ya kafa tarihi, domin ya samu nasaran gina fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa akan mota wacce zata iya tuka kanta
Allah Mai iko!

Sanannen kamfanin kera mota na duniya dake Kasar Burtaniya wato "Jaguar Land Rover" sun bawa Dr. Idris Ahmed kwangila tun kusan shekara daya da ya gabata a karkashin Kamfaninsa mai suna "Tecomex  Forensics Ltd" domin yayi aikin gina musu fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa a cikin mota ta yanda ba za'a iya yiwa motar kutse (hacking) ba, wacce zata iya tuka kanta taje ko'ina ta dawo ba tare da direba ba.
Allah ya bashi saa


 Kusan watanni 10 da suka gabata wani Lokaci da yamma Dr Idris Ahmed ya kirani a waya lokacin ya dauki lokaci mai tsawo bai hau online ba, yake sanar dani kwangilar da wannan kamfanin kera motoci ya bashi, amma yace min kada na sanar da kowa, a Kasar turai fa jama'a, 'dan Nigeria suka nema suka bashi wannan kwangila saboda ilminsa a harkon samar da tsaro wa na'ura mai Kwakwalwa

Allah Ya jikan Malam Albaniy Zaria Masanin na'ura mai kwakwalwa, wani lokaci Malam Albaniy Zaria yana gabatar da Lecture mai taken DUNIYAR ALJANU DA SHAIDANU lokacin da Malam yazo yana bayanin kwarewar da Aljanu suke dashi akan fasaha, sai da Malam Albaniy ya kawo bayanin cewa yanzu haka turawa suna nan suna tunanin yadda zasu kirkiri wata mota mai fasaha ta yadda zata iya tuka kanta, a aiketa taje ta dawo ba tare da direba ba, tsarki ya tabbata ga Allah, wato kamar Malam Albaniy Zaria yana mana ishara Dr. Idris Ahmed ne, yau abin ya zama gaskiya, Allah Ka jikan Malam Albaniy Zaria

Muna alfahari da kai Maigidana Dr Idris Ahmed Allah Ya kara maka fasaha
Muna fatan Allah Ya sa duniya ta cigaba da amfana da rayuwarka Amin.
Daga Datti assalafy. 

YADDA SOJOJIN NIGERIA KE JIGILAR KAYAN ZABEN 2019 A CIKIN JIRGI

SHIRI DOMIN ZABE

Daren jiya Litinin Rundinar sojin saman Nigeria ta fara jigilar kayanzabe daga birnin tarayya Abuja zuwa jihohin Kasarmu Nigeria gabaki daya

Jama'a a tanadi katin zabe, a gujewa duk wani mataki na tayar da hankali, abi dokokin hukumar zabe da na 'yan sanda, a baiwa jami'an tsaro da ma'aikatan zabe cikakken hadin kai
Saboda wannan zabe Na Wannan shekara ya sha ban ban da ko wane zabe Akwai dokoki da dama.

Muna fatan Allah Ya sa ayi zabe lafiya a kammala cikin nasara Amin.
Allah ya zaba muna shugaba Na Kwarai.

YADDA ZAKA BUDA E-MAIL ACCOUNT DA WAYARKA YANZU.

assalamu alaikum
Kamar yadda kuka sani cewa Wannan website Mai albarka yana kawomaku abunda ya shafi internet, to Yanzu ma ya kawomaku yadda mutum zai buda e-mail account da wayarsa cikin muntuna biyar ba tare da yaje wurin masu computer ba
Na farko ya zama wayyaraka Tana da data,sai abu na biyu ya zama layin da zaka amfani da shi yana kusa  .
Bayan mutum ya shiga link Na G-mail Account Wanda zan kawo Daga baya
Sai ya cika sunan sa na farko shine first name Misali abdulazez, sai last name shine sunan baba da kaka,
Bayan Nan sai username ma'ana sunan da kakeso G-mail account dinka ya kasance misali ausodangi@G-mail.com  Amma ba sai ka sa @gmail.com ba  su zasu samaka,
Bayan kasaka idan bai yiba kana iya Kara wasu numbobi a baya Misali abdulazez21@mail.com, bayan kasaka username sai ka saka password kamar  number takwas idan ka saka sai ka kara shiga cikin confirm Ka saka wannan password da kasa a farko, Daga nan sai ka Dana next bayan ya gama login sai ka saka phone number maana numberka,bayan Ka saka zasu turama wasu numbobi (verification code) sai ka saka su cikin box din Mai dauke da (G)  bayan Nan sai ka saka shekarun haihuwa misali :1--1--1999 Daga Nan Ka danna next shike nan sai ka danna ask me letter, shi kenan ka buda G-mail account,
Domin budewa Yanzu sai Ka Danna wannan link dake kasa
https://accounts.google.com/signup/v2/webcreateaccount?hl=en-GB&flowName=GlifWebSignIn&flowEntry=SignUp
Idan Akwai mai rambaya zai iya kiran 09060539877
Mun gode. 

Monday, February 11, 2019

KARATUN LITAFIN BULUGUL MURAM TAREDA NAIBIN MASALACIN UMAR IBN ABDULAZEZ.

KARATUN BULUGHUL MARAM MIN ADILLAT AL-AHKAM

Yau Lahadi 5th Jimada Thani, 1440 AH daidai da 10th February, 2019

Daga Masjid Umar Ibn AbdulAziz (Masallacin Gardner) Gaggaren Kwata, Gusau.

Time: Tsakanin Magariba da Isha'i

Tare da 👉🏾 Sheikh Abdullahi Mohammad Zurmi Na'ibi (Hafizahullah)
Domin saukar da wannan karatu acikin Wayyarka sai ka shiga Wannan link dake kasa


Ayi sauraro lafiya
👇👇👇

https://kiwi6.com/file/ueh6apxnr

Saturday, February 9, 2019

KARATUN LITAFIN SIYASATUL SHARIYA FI ISLAHIL RA'E WA RA'EEYA. TAREDA SHEKH USMAN MUHAMMAD SODANGI RAE'S

KARATUN SIYASATUL SHAR'IYYA FI ISLAHIL RA'E WA RA'EEYA

Yau Jummu'at 3rd Jimada Thani,1440 AH daidai da 8th February, 2019

Daga Masjid Abdullahi Ibn Abbas (Masallacin Maryam Qur'an) GRA, Gusau

Time: Bayan Sallah Magriba zuwa Isha'i

Tare da 👉🏾 Sheikh Usman Ibn Muhammad Sodangi (Hafizahullah)

Ayi sauraro lafiya
👇🏿👇🏽👇🏿

https://kiwi6.com/file/rfwu2qyxll

Dowload Audio )MUHADARA MAI TAKEN MATSAYIN AL QURANI MAI GIRMA DA KUNA MUSIBAR DA ZATA CIMMA DUK WANDA WULAKANTASHI TARE DA SHEKH AHMAD IBN UMAR KANOMA

MUHADARA ! MUHADARA !!!

Yau Jummu'a 3rd Jimada Thani, 1440 AH daidai da 8th February, 2019 a nan Masjid Umar Ibn Khadab byepass Gusau

Maudhu'i: Matsayin Al Qur'ani mai girman da gare shi da musibar da zata cimma duk wanda ya wulakanshi.

Mai gabatarwa: Sheikh Ahmad Ibn Umar Kanoma Abu Abdullahi tare Malam Aminu Aliyu Gusau (Hafizahullah) da Sheikh Dr Aliyu M Jangebe (Hafizahullah) da Dr Muhammad Rabi'u Shehu Na'ibi (Hafizahullah) da Sheikh Bashir Isah (Hafizahullah)

Allah Ya isarmana ga duk wadanda ke wulakanta Al Qur'aninka mai girma, Allah kada ka biya masu da dukkan bukatunsu. Amin

Ayi saurare lafiya.
Domin saukar da wannan karatu sai ka shiga Wannan link dake kasa


👇👇👇👇👇
https://kiwi6.com/file/338pq0q2g9Tuesday, February 5, 2019

DOWLOAND) KARATUN LITAFIN BULUGUL MURAM TARE DA NA'IBIN MASALACIN UMAR IBN ABDULAZEZ (GADINA GUSAU)

KARATUN BULUGHUL MARAM MIN ADILLAT AL-AHKAM

Yau Lahadi 27th Jimada Auwal, 1440 AH daidai da 3rd February, 2019

Daga Masjid Umar Ibn AbdulAziz (Masallacin Gardner) Gaggaren Kwata, Gusau.

Time: Tsakanin Magariba da Isha'i

Tare da👉🏾 Sheikh Abdullahi Mohammad Zurmi Na'ibi (Hafizahullah)
Domin saukar da wannan karatu sai ka shiga Wannan link dake kasa domin saukar da wannan karatu
https://kiwi6.com/file/2b93gvwyw1

Ayi sauraro lafiya
👇🏿👇🏽👇🏿

Saturday, February 2, 2019

Download audio) KARATUN LITTAFIN SIYASAYUL SHAR'IYYA FI ISLAHIL RA'E WA RA'EEYA

KARATUN SIYASATUL SHAR'IYYA FI ISLAHIL RA'E WA RA'EEYA

Yau Jummu'at 25th Jimada Auwal,1440 AH daidai da 1st February, 2019

Daga Masjid Abdullahi Ibn Abbas (Masallacin Maryam Qur'an) GRA, Gusau

Time: Bayan Sallah Magriba zuwa Isha'i 

Tare da 👉🏾 Sheikh Abubakar Ibn Muhammad Sodangi (Hafizahullah)
Domin saukar da wannan karatu sai kashiga wannan link dake kasa
Ayi sauraro lafiya 
👇🏿👇🏽👇

Dowloand) karatun litafin Tarbiyatul Aulad Na shekh abubakar Muhammad sodangi algusawiy a masalacin umar ibn abdulazez (GAdina) 26/5/1440# 2/2/2019

KARATUN TARBIYATUL AULAD FI ƊIYA'U KITAB WAS SUNNAH

Yau Assabar  26th Jimada Auwal, 1440 AH daidai da 2nd February, 2019

Babin hakkin na tara akan iyaye sukoyawa diyansu Mata sa Hijabi tun suna da shekara bakwai (7).

Daga Masjid Umar Ibn Abdul-Aziz (Masallacin Gardner) Gaggaren Kwata, Gusau.

Time: Tsakanin Magariba da Isha'i

Tare da👉🏾 Sheikh Abubakar Ibn Muhammad Sodangi (Hafizahullah)
Domin saukar da wannan karatu sai ka shiga Wannan link dake kasa. 
Ayi sauraro lafiya 
👇🏿👇🏽👇🏿


Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Minene z-sip program