Sunday, February 24, 2019

AN KAMMALA FASSARAR LITTAFAN PHYSICS, CHEMISTRY, MATHEMATHICS ZUWA HARSHEN HAUSA.Asslam alaikum 
Muna godiya ga Allah subahanahu     wata'ala,
A yau insha Allah zamuyi magana Akan kamala fasssrar littafan chemistry physics, mathematics zuwa harshen hausa Wanda cibiyar bincike kan harsunan Nigeria da fasssra da hikimomin Al umma dake jami'ar bayero kano  university (B U K), 
Wannan cibiya ta dake bayero university dake birnin kano tayi nasarar bugawa tare da fassara littafan kimiya guda takwas zuwa Yaren Hausa saboda daliban firamare da kuma karamar sikandarari (junior section) da kuma babbar sakandari (senior section) saboda dalibai yan yankin arewacin Nigeria, 
Shugaban Wannan cibiya farfesa Aliyu mua'zu yace littafan sun hada da :
1,kimiya da fasaha Don makarantun firamare,litafi Na daya zuwa na ukku 
2,Lisafi don kananan makaratun sakandari, Littafi Na daya zuwa na ukku, 
3,Fizis (physics) don Mayan makarantun sakandari, 
4,Kyamistiri (Chemistry) don manyan makaratun sakandari .
Waddanan Sune littafan da aka fassara zuwa Hausa. 
Haka kuma Alokacin gudanar da wannan aiki shima farfesa Mu'azu yace sunyi amfani ne da tsarin karantawa Na kasa (National curriculum) tareda taimakawar aboakan aikinsu na faculty of education da kuma faculty of science, 
A karshe kungiyar ta arewa (sof)  Tana Kira ga dukkanin hukumomomin jihohi Dana tarayya da su amince da yin amfani da wadannan littafan a makarantunmu Don haifar da kwararun likitoci da injiniyoyi da sauransu. 
Ubangiji Allah yasaka masu da Alheri.

No comments:

Post a Comment

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Minene z-sip program