Tuesday, February 12, 2019

TSOKACINA A KAN KALAMAN SEN: RABI'U KWANKWASO (DR IBRAHIN ILYASU.


Tsokacina A Kan Kalaman Sen. Rabiu Kwankwaso !

Bayan na saurari munanan Kalaman Senator Rabiu Kwankwaso a kan wasu Malaman Sunnah da ya samu sabani da su, ina da tsokaci kamar haka:

1. Da farko, ina so me karatu ya sani, bani da personal sabani da Kwankwaso, kuma ina da dalibai da yawa da aminai masu bin kwankwasiyyah, wasu ma na kusa da shi ne sosai, wasu ma har abinci suna ci tare. Hakanan bani da wata alaka da Gov Ganduje ko Mal Salihu Takai, ko da yake ina da dalibai da abokai zagaye da su.

2. Lallai Senator Kwankwaso Shugabane Jarumi (Strategist), a matsayinsa na tsohon Gwamna har sau biyu a Kano, wanda ya rike manyan mukamai a tarayya, babban dan siyasa ne me dinbin mabiya da tasiri a jaharsa da ma kasa. Jagora ne da ya taimaki yayan talakawa musamman  a cikin mulkinsa karo na biyo, akwai dalibaina da yawa wadanda ba 'ya'yan kowa ba ne amma sun samu damar karo karatu a Malaysia da wasu kasashen duniya a dalilinsa, wannan abu ne da ya kamata a yaba masa a kai.

3. Sai dai kuma lokaci-lokaci Sen. Kwankwaso ya kan saki baki ya furta wasu kalamai a zahiri na Izgilanci ne ga Sunnah dama  addini gaba daya: misali lafuzzan da yayi kwanan a kan Gemu, da Dage Wando, saboda ya samu sabani da wasu Malaman Izala. Babu shakka lafuzzan bai kamata su fito daga bakin Shugaba me tarbiyyar alummah ba!

4. Idan Kwankwaso yana yin raddi ne ga Malaman da ya samu sabani da su, me ya hana ya tsaya akansu su kadai, don me ya tsallaka yayiwa Gemu da dage Wando izgilanci.

5. Babu shakka Masu Kishin addini za su ga wannan  izgili  ne ga Sunnah da ma addini gaba daya. A baya ma, Kwankwaso yayi sakin baki ga Annabi SAW da mahaddata Qurani, lokacin yana kan mulki.

6.Hakika, duk yanda kaso ka kyautata wa Kwankwaso zato ze yi wuya kace Malaman addini suna da girma a idonsa, kasancewar shine Gwamna na farko da ya dauko Dan Siyasa yaronsa  mara alaka da ilmin addini kwata-kwata, ya bashi me bada shawara akan harkar addini, a gari kamar Kano. Hakika, wannan cin fuska ne ga addini da Malaman addini. Ko da yake Gov Ganduje ya ci gaba da rikeshi domin biyan bukatarsa ta siyasa.

7. Ba Kwankwaso ka dai ba, so da yawa, wasu mutane kan jefi Malaman addini da Kalmar "kwadayi". Sai dai an manta, yanayin Kasarmu na "secularism" da rashin mutunta addini da masu yi masa hidima yasa malamai kan shiga wahala saboda rashin albashi daga Gwamnati da kuma tallafi daga mabiya, duk da cewa lokacinsu da zasu je su nemi abinci shi suka sadaukar suka baiwa alumma, wajen; Jagoranci, Limanci, Khutubah, lecture, Programs, a Radio da sauransu. Sabanin a sauran kasashen duniya inda Malamin addini ke samun cikakkiyar kulawa, Gaida, albashi, mota, da sauransu. Amma anan dan siyasa da ya dau kudin alumma ya gina kansa da iyalinsa, da sauran ma rasa gane alamura, su ne zasu rinka yiwa Malamai gori, domin sun basu kudi, tunda su ba yan kasa bane, basu da hakki a dukiyar kasa.

8. Lallai akwai Malamai na Izala da na Dariqah masu rashin Qana'a da wadatar zuci wadanda suke abinda bai daceba na kwadayi da zubar da kimar ilmi, ya wajjaba su daina su martaba ilminsu da darajarsu.
 ولو ان اهل العلم صانوه صانهم. .. ولو عظموه في النفوس افظما

9. Tabbas Kwankwaso ya lura mabiyan Malaman Dariqah sun fi zafi da karsashi  wajen  kare Malamansu shi yasa bai taba yi musu irin wannan kakkausan sukan ba. Daliban Sunnah kalubalenku!

10. Akwai fitattun 'Yan Siyasa irinsu Musa Ilyasu Kwankwaso wadanda suka shahara wajen cin Mutuncin Sen Kwankwaso a kullum a Radio, da kuma shahararrun mawaka irinsu Rarara Wanda a wakarsa ya ke cin mutuncin Kwankwaso da kalmomi masu muni irinsu: Tsula, Biri, Jan Gwalagwada. Abin mamaki ban taba jin yafito yai musu kakkausan raddi ba, sai Malaman sunnah.

11. Ina bada shawara ga Sen Kwankwaso ya tuba ga Allah kuma ya nemi afuwa kuma ya shirya tsakaninsa da Malaman Sunnah, sannan ya rinka tauna magana Kafin ya fade ta, a matsayinsa na jagora me dinbin Mabiya. Makusantansa su rinka nuna masa hadarin yin tabargaza da izgilanci ga addini domin kafircine kuma muna funci ne.

قل ابالله وآياته ورسوله كنتم تستهزءون لاتعتذروا قد كفرتم بعد ايمنكم

12. Daga karshe, ko waye mutum,  komai daukakarsa in dai zai taba addini, to Allah zai yi maganinsa, domin shine zai shiga fadan. Kuma bukatar me irin wannan ba zata biya ba, kuma makiyansa sai sunga bayansa.

من عادى ليا فد.آذنته بالحرب

إن الله يدافع عن الذين آمنوا إن الله لايحب كل خوان كفور.
أذن للذين يقتلون بأنهم ظلموا وإن الله على نصرهم لقدير

Allah muna rokonka ka tsare mana imaninmu.

Dr Ibrahim Ilyasu
12/2/2019

No comments:

Post a Comment

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Hon Kabiru Amadu mai Palace yayi Babban Albishir Ga wadanda suka samu z-sip program