Friday, September 6, 2019

Minene z-sip program

ASSALAMU ALAIKUMSalam,...
TAKAITACCHEN BAYANI KAN ZASIP.
Tsari ne aka shirya shi irin tsari na N-Power, tallafi ne ba aiki bane, ba fansho ba Giratuti. Gaba daya Mutu 3800 zaa dauka, matasa Maza da Mata Wanda duk wata Mai girma Gwamna Zai basu 10,000.
Haka kowache karamar hukuma Tanada Coordinators da Supervisors Wanda Mai girma Gwamna ya Aminta da duk wata zai basu 100,000 kowannen su har su Goma 14.
Haka kowache mazaba na da coordinator Guda guda Wanda kowannane su zaa basu 50,000. Sanna akwai kwamiti na jiha Wanda zasu kula da tsarin yadda aikin zai gudana, Sanna akwai kwamitin mu na rikon kwarya Wanda idan mun kammala zamu sakar ma coordinators su chi gaba da gudanar da shirin.
Kowache karamar hukuma zaa iya samun forms ta hannun wadannan wurare domin sune aka raba forms tsakanin su dai dai Gwargwado;-
PDP LG HQtres
Senators
Reps
State Assembly
Traditional Institutions
G8
Stakeholders
Sannan Anbude website (www.z-sip.com.ng) ga Wanda baida hanya ga duka wadannan da aka ba forms shikuma yachika da wayar shi ko kuma yaje gurin da akwai cafe ya chika. Ranar jumaa zaa kammala raba forms da chikewa online.
Zaafitar da sunayen wadanda sukayi nasara chikin sati Mai zuwa, idan kwamiti ya kammala shirye shirye zai kirasu domin tantanchewa.
Baa sayar da form na Z-Sip sai dai duk cafe dakaje chikewa suna da hakkin su chaje ka yadda suke tsarin su.
Kuma ba CAFE Guda kawai ke iya chikewa ba ko ina kaje duk daya ne ko kuma da wayar ka duk zaiyi.
Muna godiya ga Mai girma Gwamna Bello Matawalle domin taimakon Matasa.
Allah ba Mai rabo saa
Allah shi yabbamu
Allah mungode.
Daga Abdulazez Umar Sodangi

No comments:

Post a Comment

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Hon Kabiru Amadu mai Palace yayi Babban Albishir Ga wadanda suka samu z-sip program