Wednesday, November 27, 2019

Hon Kabiru Amadu mai Palace yayi Babban Albishir Ga wadanda suka samu z-sip program


MUN GAMSU MATUKAR GASKE DA SHIRIN ZAMFARA SOCIAL INTERVENTION PROGRAM (Z-SIP)

Allah shi zai bamu blogger team

Al'ummar jahar Zamfara yau cike suke da farin ciki da annashuwa da jin albishir daga bakin gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun a kan yunkurinsa na tabbatar ya rage radadin talauci dake addabar al'ummar jahar nan, la'akari da yadda tsohuwar gwamnatin data shude tayima ma'aikatan wannan jahar rikon sakainar kashi.

Gwamna matawalle dayake jawabi a wurin kaddamar da wannan shirin ya tabbatar da cewa da farko sun tsara cewa zasu dauki mutun dubu uku da dari takwas ne (3800) domin amfana da wannan shirin, amma daga baya suka kara adadin yawan mutanen yakai kimanin mutun dubu biyar da dari shida (8'692) la'akari da yadda al'ummar wannan jahar suke ciki badan komai ba, sai dan irin musgunawa da takura da mutane suka samu daga tsohuwar gwamnatin data shude.

Kazalika sakataren wannan Kwamitin Hon Kabiru Amadu Mai Palace Dan majalisa mai wakiltar Gusau da Tsafe yayi wani albishir ga al'ummar da suka samu nasara aka tan-tancesu da cewa InshaAllah ranar juma'a dinnan 29-11-2019 kowa zai fara jin Alert daga asusun ajiyarshi, daga bisani shima gwamna matawalle yakara jaddada hakan a dai-dai lokacin dayake jawabi a wurin taron.

Da wannan muke rokon ubangiji Allah ya cigaba da dafama gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, su kuma wadanda zasu amfana da wannan shirin Allah yasa yazama shine silar yin arzikinsu.

Allah shi zai bamu blogger team.
27-11-2019

Bincike,Tarihi da kuma wayarwa Akan internet hadi da tarihin manyan Malamai da kuma fadakarwa.

Hon Kabiru Amadu mai Palace yayi Babban Albishir Ga wadanda suka samu z-sip program